HAKAN BAYA TABA ZAMA HANYAR GYARA!
Manzon Allah-tsira da aminci su ƙara tabbata a gareshi yana cewa:
(( ﻣﻦ ﺃﺭﺍﺩ ﺃﻥ ﻳﻨﺼﺢ ﻟﺴﻠﻄﺎﻥ بأمر ﻓﻼ ﻳُﺒْﺪِ ﻟﻪ ﻋﻼﻧﻴﺔ، ﻭﻟﻜﻦ ﻟﻴﺄﺧﺬ ﺑﻴﺪﻩ فليخو به، فإن قبل منه فذاك، وإلّا كان قد أدّى الذي عليه له ))
(( DUK WANDA YASO YAYI NASIHA GA SHUGABA TO KADA YA BAYYANAR DA NASIHARSA A FILI, SAIDAI YAYI RIƘO DA HANNUNSA YA KEBANCE DASHI, IDAN YA KARƁA DAGA GARESHI TO DAMA HAKA AKESO, AMMA IDAN BAI KARƁA BA TO SHI YA SAUKE HAƘƘIN DA YAKE KANSA ))
Daga wannan hadeethi zamu iya fahimta cewa:
Baya halalta ga Malami, limami ko mai wa'azi ya haye kan minbarin juma'ah ko minbarin wa'azi yana tada jijiyoyin wuya wajen ambato aibi da laifukan shuwagabannin al'ummah!
Babu maslaha cikin haka kuma babu hikima ko mithqala zarrah.
Daga :
Abul-Mustapha Al-athary
May 13, 2016

Comments
Post a Comment