Skip to main content

IDAN ƁERA NADA SATA..



JAGORA DA WANDA AKE JAGORANTA

 Allah madaukakin sarki ya raba ayyuka kuma yaba kowa nasa:

1- Shuwagabanni su riƙe nasu suyi ƙoƙarin saukewa, domin Allah zai tambayesu game da nauyin da ya dora masu. 

2- Waɗanda ake shugabanta su riƙe nasu suyi ƙoƙarin saukewa, domin Allah zai tambayesu game da nauyin da ya ɗora masu. 

Kada wani ya shiga aikin wani! 

Duk wanda ya shiga aikin wani, ko yayi sakaci wajen zartar da nasa aikin, lallai ya saɓawa Allah maɗaukakin sarki.

Shugabanci abune mai tsananin wahala, kuma lallai akwai hisabi tsakanin shuwagabanni da mabiya. 

Duk wani shugaba wanda yayi amfani da jagorancinsa ko ƙarfin mulkinsa ya muzgunawa waɗanda yake jagoranta, lallai zai tarar da hukuncinsa a wajen ubangijinsa. 

Tabbas haƙƙi ne ga shugaba ya tsarewa al'ummarsa ababe kamar haka:

 (1) Rayukansu 

 (2) Addininsu

 (3) Dukiyoyinsu

 (4) Hankulansu 

 (5) Mutuncinsu

Da sauransu.  

Haƙiƙa Allah maɗaukakin sarki ya wajabta kyautatawa akan komai, shine ya hukunta jagorancinsu, shine kuma zai bincike su yayi masu hukunci cikin sakancinsu, ko kuma ya saka masu da alkhairi game da jajurcewarsu cikin sauke nauyin da ya rataya masu.

Idan muka waiwaya ɗaya ɓangaren zamu tarar cewa :

Allah maɗaukakin sarki bai sahhalewa wani mabiyi yayi taratsi da fito na fito ga shuwagabanni ba, kuma ko kaɗan bai bada dama ga waɗanda ake jagoranta su zama masu neman haƙƙinsu a wajen jagororinsu ta hanyar bore, nuna isa ko hargowa ga shuwagabanninsu ba 

Saidai ya ɗora masu nauye-nauye wajen mu'amalantar shuwagabanninsu kamar haka:

(1) Yi masu ɗa'a cikin dukkanin abinda yake daidai

(2) Haquri game da zaluncinsu idan azzalumai ne. 

(3) Yin nasiha garesu a boye ta hanyar girmamawa da tausasawa.

(4) Yi masu addu'ar gyaruwa da shiriya da samun nasara a cikin jagorancinsu.

Idan ya zamanto akwai wasu haƙƙoƙinsu da suke ganin jagororinsu sun gaza sauke masu, sai su roƙi Allah ya ƙwato masu haƙƙinsu ta hanyar kyawawan addu'o'i.

Babu shakka akwai buƙatar mu kyautata domin mu sami yardar Allah, mu daure muyi riqo da tafarki madaidaici domin samun tsira duniya da lahira. 

Allah ya datar damu da abinda yake so kuma ya yarda dashi. 

 Daga:

 Abul-Mustapha Al-athary

June 21, 2020.

Comments

Popular posts from this blog

INDAI HAR ALLAH YA ƘADDARA..

  BABU MAI HANYAR TSEREWA ƘADDARA!   Allah maɗaukakin sarki shi yayi halitta kuma ya ƙaddari duk abinda zai wakana gareta akan tsarin da yaso, a cikin lokacin da yaso, babu kuma wanda ke da ikon samar da wanin tasgaro ko daƙile afkuwar abinda yayi nufin afkuwarsa.  Kenan, babu wajen tsira daga wani bala'i idan Allah ya ƙaddarasa ga bayinsa ! Don haka idan taka jarabtar ta iso gareka sai ka sanyawa zuciyarka natsuwa kuma kace : Allah ne ya ƙaddara kuma shi keda ikon aikata abinda yaso!  Ka tuna cewa lallai duk wanda yace shi me imani ne to ai dole yayi guzuri na juriya game da musibun da za'a jarabci imaninsa dasu. Don haka sai mu fuskanci jarabawarmu da karbabbiya kuma yardajjiyar fuskanta, domin duk wanda ya miƙa wuya ga Allah, Allah yana shiryatar da zuciyarsa zuwa ga rabauta. Allah maɗaukakin sarki ya yaye mana dukkanin ƙunci, kuma ya bamu ikon cinye kowace irin jarabawar da yake gwada imanin bayinsa da ita.  Daga : Abul-Mustapha Al-athary  September 5,...

KU ZURFAFA NAZARI DAI..

HAKAN BAYA TABA ZAMA HANYAR GYARA! Manzon Allah-tsira da aminci su ƙara tabbata a gareshi yana cewa: (( ﻣﻦ ﺃﺭﺍﺩ ﺃﻥ ﻳﻨﺼﺢ ﻟﺴﻠﻄﺎﻥ بأمر ﻓﻼ ﻳُﺒْﺪِ ﻟﻪ ﻋﻼﻧﻴﺔ، ﻭﻟﻜﻦ ﻟﻴﺄﺧﺬ ﺑﻴﺪﻩ فليخو به، فإن قبل منه فذاك، وإلّا كان قد أدّى الذي عليه له )) (( DUK WANDA YASO YAYI NASIHA GA SHUGABA TO KADA YA BAYYANAR DA NASIHARSA A FILI, SAIDAI YAYI RIƘO DA HANNUNSA YA KEBANCE DASHI, IDAN YA KARƁA DAGA GARESHI TO DAMA HAKA AKESO, AMMA IDAN BAI KARƁA BA TO SHI YA SAUKE HAƘƘIN DA YAKE KANSA )) Daga wannan hadeethi zamu iya fahimta cewa:  Baya halalta ga Malami, limami ko mai wa'azi ya haye kan minbarin juma'ah ko minbarin wa'azi yana tada jijiyoyin wuya wajen ambato aibi da laifukan shuwagabannin al'ummah! Babu maslaha cikin haka kuma babu hikima ko mithqala zarrah. Daga : Abul-Mustapha Al-athary May 13, 2016