SANIN SUNAYEN ALLAH DA SIFFOFINSA SUNE ALJANNAR DUNIYA ! Idan bawa yasan sunayen Allah da siffofinsa, kuma yayi ƙoƙarin roƙonsa dasu, yayi ƙoƙari wajen bautar ubangijinsa da ababen da suka ƙunsa, to tabbas wannan bawa ya sami aljannar duniya wacce duk wanda bai shigeta ba tofa bashi ba shiga ta lahira . Domin kuwa, mafi girman rabauta da tsira acikin duniya shine bawa yasan ubangijinsa, kuma yasoshi, ya kusanceshi. Wannan shine farko abinda Allah-maɗaukakin sarki-ya ambata na daga ni'imomin da zai gabatarwa ma'abota aljannah. Allah maɗaukakin sarki yana cewa: “DA WAƊANDA SUKA RIGA, MADALLA DA WAƊANDA SUKA RIGA, WAƊANNAN SUNE MAKUSANTA A CIKIN ALJANNA TA NI'IMAH” [Al-waƙi'ah/10-12] Sai Allah-maɗaukakin sarki ya fara ambaton kusancinsu kafin ya ambaci aljannah, kuma kafin ya ambaci dukkanin ababen da ya tanadar masu cikinta, na abinci ko abin sha ko mata da sauran ababen ni'ima. Allah maɗaukakin sarki ya albarkacemu da ribatar ilimi mai amfani Daga : Abul-Mustaph...
Nagartaccen ilimi daga asali cikin sauƙi ba ƙunci. Tatacciyar tarbiyya mai samar da daddaɗan yanayi a zuci. Tsaftatacciyar rayuwa mai haifar da walwala cikin ƴanci.