BABU MAI HANYAR TSEREWA ƘADDARA! Allah maɗaukakin sarki shi yayi halitta kuma ya ƙaddari duk abinda zai wakana gareta akan tsarin da yaso, a cikin lokacin da yaso, babu kuma wanda ke da ikon samar da wanin tasgaro ko daƙile afkuwar abinda yayi nufin afkuwarsa. Kenan, babu wajen tsira daga wani bala'i idan Allah ya ƙaddarasa ga bayinsa ! Don haka idan taka jarabtar ta iso gareka sai ka sanyawa zuciyarka natsuwa kuma kace : Allah ne ya ƙaddara kuma shi keda ikon aikata abinda yaso! Ka tuna cewa lallai duk wanda yace shi me imani ne to ai dole yayi guzuri na juriya game da musibun da za'a jarabci imaninsa dasu. Don haka sai mu fuskanci jarabawarmu da karbabbiya kuma yardajjiyar fuskanta, domin duk wanda ya miƙa wuya ga Allah, Allah yana shiryatar da zuciyarsa zuwa ga rabauta. Allah maɗaukakin sarki ya yaye mana dukkanin ƙunci, kuma ya bamu ikon cinye kowace irin jarabawar da yake gwada imanin bayinsa da ita. Daga : Abul-Mustapha Al-athary September 5,...
AL-ATHARY TV
Nagartaccen ilimi daga asali cikin sauƙi ba ƙunci. Tatacciyar tarbiyya mai samar da daddaɗan yanayi a zuci. Tsaftatacciyar rayuwa mai haifar da walwala cikin ƴanci.